Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ?asar za ta kashe naira biliyan 22.44 wajen ciyar da ?aurarru a gidajen yarin da ke fadin ?asar.
Gidan talbijin na Channels ya ruwaito Babban Sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Dr Shuaib Belgore na bayyana haka yayin wani babban taro na kwana biyu a kan rage cunkoso da gyara halin ?aurarru a Abuja.
Dr Shuaib Belgore ya ce ku?in an sanya su a cikin dokar kasafin ku?in shekara ta 2023.
Ya ce ana samun ?aruwar mutanen da ake da su a gidan yari babu ?a??autawa, inda ?aurarrun da ke zaman jiran shari’a suka kai kashi 80%.
A cewarsa, akwai gidan yari 244 a fa?in Najeriya, inda ake tsare da mutum 75,507, abin da ya kawo cunkoso a cikin 82 daga cikinsu.
Haka zalika, adadin maza da ake tsare da su a gidajen yarin Najeriya sun kai 73,821, sai kuma mata 1,686.
Dr Shuaib Belgore ya ce a cikin fursunoni 75,507 da ake da su, 52,436 suna jiran shari’a yayin da 23,071 kuma suke zaman hukuncin da aka yanke musu.
Akwai kuma fursunoni 3,322 da aka yankewa hukuncin kisa, su ma da ake tsare da su.