Babu Inda Na Yanke Jiki Na Fadi – Tsohon Ministan Lantarki

A zantawar da BBC Hausa ta yi da tsohon Ministan Lantarki Sale Mamman ta wayar tarho, ya bayyana yanayin da yake ciki a yanzu.

Tsohon ministan ya ce dama yana fama da rashin lafiya tun a ƙarshen makon da ya gabata.

“Tun kafin a sanar da wannan mataki dama ba ni da lafiya, don ko ofis ban je ba tun farkon makon nan.”

Tsohon ministan ya dama ya dade ba shi da isasshiyar lafiya don yana yawan zuwa ganin likita ma akai-akai.

“To a jiya Laraba da yau Alhamis ma na koma asibiti don sake duba ni, kuma likita ya ce min ina bukatar hutu don haka na zauna waje guda don na huta,” in ji shi.

A yanzu dai tsohon Ministan Lantarkin ya ce ba a kwance yake a asibiti ba kamar yadda ake yadawa, sai dai kuma ba ya gidansa.

“Na samu waje ne mai nutsuwa ina hutawa da shan magani kamar yadda likita ya ba da shawara. Ban zauna a gida ba saboda tururuwar ‘yan jaje za ta hana ni hutawar da samun sauki kan kari.

“Amma kuma ba kwantar da ni aka yi a asibiti ba, sannan ban yanke jiki na fadi ba kamar yadda ake ta yadawa.”

Sale Mamman ya kuma ce a ranar Litinin da daddare Shugaba Buhari ya kira shi a waya ya sanar da shi batun sauke su din, tare da yi masa godiya kan irin gudunmowar da ya bayar a gwamnatinsa.

Ya ce a saninsa ba wai wani laifi ya yi ba da ya sa shugaban ya sauke shi, “dama ko ba a sauke ni yanzu ba dole na sauka nan da shekara biyu,” in ji shi.

Sannan ya yi waiwaye kan shekarar 2019 lokacin da aka ba shi minsitan, inda ya ce ba nema ya yi ba, kiransa aka yi aka ce ya tura takardunsa wato (CV), “kuma cikin awa biyu da turawar aka ce an nada ni minista.”

Sale Mamman, wanda dan asalin Jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya ne ya ce yana alfahari da irin ayyukan da ya yi a lokacin da yake kan kujerar, musamman sauye-sauyen da ya yi a harkar wutar lantarki a Mambila.

“Kuma ni na raya jam’iyyar APC da ta kusa kai wa kasa a Jihar Taraba,” in ji shi.

A karshe ya ce yana da burin ci gaba da harkokin siyasa kuma zai koma siyasa ka’in da na’in.

Labarai Makamanta

Leave a Reply