A Kasuwa Nake Ga Duk Mai Bukata – Momi Gombe

Shahararriyar Jarumar Finafinan Hausa Maimuna Abubakar wadda aka fi sani da suna Momi Gombe ta bayyana cewar a halin yanzu ba tada da wani buri wanda ya wuce yin aure da raya sunnar ma’aiki.

Momi Gombe ta bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da gidan Rediyon BBC Hausa ya yi da ita cikin shirin “Daga Bakin Mai Ita”.

A cewar Jarumar tabbas ta taɓa yin aure ita Bazawara ce amma ba ta haihu, a halin yanzu a kasuwa nake ga dukkanin mai bukatar aure.

Sai dai Jarumar ta ƙaryata maganar da wasu ke yaɗawa na cewar tana soyayya da sanannen Mawaƙin nan Hamisu Breaker, inda ta ce mutunci ne a tsakanin su kawai.

Momi Gombe ta kara da cewar ba za ta manta wakar Jarumar Mata da suka yi da Hamisu Breaker ba domin wakar ta sanya ta yi fice sosai har wasu ke kiranta da sunan Momi Jarumar Mata.

Labarai Makamanta

Leave a Reply