Zan Haskaka Najeriya Idan Na Lashe Zabe – Atiku

Ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha alwashin fidda Najeriya daga kungurmin duhun da take ciki idan aka zabe shi a zaben 2023.

Ya bayyana haka ne yayin da yake magana a wani taron kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Legas (LCCI) ta 2022 da aka yi a a birnin Ikko na Jihar Legas.

Da yake bayyana kadan daga manufofinsa, ya ce ya shirya tsaf don tabbatarwa da inganta tattalin arzikin Najeriya matukar ya gaji Buhari a shekarar 2023.

A bangare guda, Atiku ya koka da yadda Najeriya ke cikin matsin tattalin arziki, kana ake samun faduwa maimakon tashi a fannin. Ya ce, daya daga cikin manufofinsa shine inganta kasa ta fannin tattalin arziki, don haka zai yi kokarin cire Najeriya daga kangin.

A cewar Atiku, Najeriya a dabaibaye take da dimbin bashi da tuni ya riga ya yi mata katutu. Ya kuma shaida cewa, Najeriya a karkashin mulkin APC bata samu wani karuwa ba illa gibin da kullum take samu a kasafin kudi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply