Inganta Tsaro: Shugaban Kasa Ya Bukaci A Sauya Dokokin Aikin Soji A Afirka

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce ya kamata Najeriya da makwabtanta da ke yankin tafkin Chadi su ƙara ƙaimi wajen sauya dokoki da ayyukan sojin ƙasashensu.

Bola Tinubu ya ce sauya dokokin aikin sojin ya zama wajibi sakamakon yadda ƙasashen yankin ke fama da ƙaruwar tashe-tashen hankula.

Yayin da yake jawabi awajen bikin yayen manyan sojoji kwas na 45 da aka gudanar kwalejin sojoji da ke Jaji a jihar Kaduna, shugaban kasar ya lissafo wasu kalubalen tsaro da ke fuskantar sojojin ƙasar da na sauran ƙasashen yankin tafkin Chadi, waɗanda ya ce suna amfani da tsoffin dokokin aikin soji.

Shugaban na Najeriya – wanda ya ƙarfafa wa ƙasashen Afirka gwiwa wajen yin aiki tare don kawar da kalubale guda da suke fuskanta – ya yaba da irin yunkurin da ƙasashen yankin tafkin Chadi ke yi na wanzar da zaman lafiya a yankin.

Ya ƙara da cewa hadin kan da ƙasashen yankin tafkin Chadin ke yi wajen yakar ayyukan ‘yan bindiga abin a yaba ne, amma yayi kira da a sauya dokokin domin kawar da barazanar da suke fuskanta

”Dole mu yi kokarin sauya dokokin aikin sojinmu. domin yakar makiyan da ke barazana ga ƙasashenmu”.

Dole mu mu sake shiri domin kawar da wannan matsala. Wannan kuma na bukatar sauyi tunani da tsare-tsare da dabarun da amuke amfani da su.

haka kuma shugaba Tinubu ya yi amfani da bikin wajen bayyana manufar tsaro da gwamnatinsa ke son cimmawa, yana mai cewa zai mayar da hankali wajen samar da tsaro da adalci da dimokradiyya da ci gaban ƙasar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply