Kaduna: Uba Sani Ya Tura Tawagar Likitoci Domin Dakile Cutar Mashako

Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya umarci ma’aikatar lafiyar jihar da ta gaggauta tura tawagar likitoci domin gudanar da bincike tare da ɗaukar matakan da suka dace kan ɓullar cutar mashaƙo a wasu yankunan jihar

Ma’aikatar lafiyar jihar ta tabbatar da bullar cutar a wasu garuruwan Kafancan da ke yankin ƙaramar hukumar Jema’a, bayan bayyanar alamomin cutar a wasu unguwanni a garin na kafancan.

Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Muhammad Lawal Shehu ya fitar, ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki matakin ne bayan samun rahotonnin ɓullar cutar tare da rasa rayuka a garuruwan.

Binciken farko da ma’aikatar lafiyar jihar ta gudanar ya nuna cewa an fara samun ɓullar cutar mashaƙo a garin na Kafancan tun farkon watan Yuli.

Sanarwar ta kuma ambato gwamnan na yaba wa hukumomin lafiyar jihar bisa ɗaukar matakan gaggawa na daƙile yaɗuwar cutar, tare da yin kira a gare ta da ta ci gaba da ƙoƙari domin yaƙar cutar a faɗin jihar.

A baya-bayan nan cutar mashaƙo na ci gaba da ɓulla a wasu jihohin ƙasar, tare da rahotonnin rasa rayuka masu yawa a wasu jihohin.

Alamomin cutar sun haɗar da wahalar numfashi, da zazzaɓi mai zafi, da tari, da kasala, da zafin maƙogoro da kuma kumburin wuya.

Hukumar lafiyar ta kuma shawarci mazauna jihar da su ɗauki matakan kariya domin kaucewa bazuwar cutar a faɗin jihar.

shawarwarin da hukumar ta bayara sun haɗar da:

  • Yawan wanke hannu da sabulu.
  • Kauce wa cuɗanya da mutanen da suka kamu da cutar
  • Rufe baki da hanci a lokacin tari ko atishawa
  • Kaurace wa makaranta ko wurin aikin idan ba ka da lafiya
  • Yin atisaye ko sassarfa domin inganta garkuwar jiki
  • Kai rahoton bullar alamomin cutar

Labarai Makamanta

Leave a Reply