Kungiyar kananan hukumomi ta kasar, NULGE ta nemi gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta yi wa ma’aikata karin albashi da abun da bai gaza kashi 300 cikin 100 na albashin da kowannensu ke karba ba.
Sai dai a wannan karon a iya cewa bukatar ma’aikatan kananan hukumomin ta ci karo da bukatar uwar kungiyar kwadago ta NLC wadda ta nemi gwamnatin Najeriyar ta yi wa ma’aikata karin kashi 200 domin rage radadin janye tallafin mai.
NULGE ta ce ta cimma matsaya ne kan karin na kashi 300 bayan taron kolin da ta yi wanda ta ce shi ne ya dace da ma’aikatanta.
Mataimakin shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Muhammad Gudaji, ya ce tun da an samu karin da ya fi na kashi 300, amma su sun ce ya kamata a kara musu albashi da kashi 300 a matsayin mafi karancin albashi.
”Shi kansa kaso 300 idan ka duba halin da aka shiga ba wani abu ba ne sai dai shi ma a yi hakuri” in ji shi.
Ya ce kofarsu a bude take domin tattaunawa da mahukunta don samun maslaha da kuma tsamo jama’a daga halin da suke ciki.
Ya ce a matsayin kananan hukumomin wadanda suka fi kusa da jama’a, sun fi yada arziki a tsakanin al’umma, don haka samun albashi mai kyau a gare su zai taimaka sosai.
”Har yanzu mun san akwai jihohin da ba su ma fara biyan Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi ba don haka wannan karon muna kira da a yi mana” in ji shi.
Ya ce idan gwamnati ta ki amsa wannan koke nasu za su kira taron mahukunta na gwamnati don tattauna mataki na gaba da ya kamata a dauka.