Yaki Na Mayar Da Hannun Agogo Baya – Fafaroma

Labarin dake shigo mana daga birnin Batikan na bayyana cewar Fafaroma Francis yayi tsokaci dangane da iftila’in yaƙi da ke faruwa yanzu haka tsakanin ƙasar Rasha da Ukraine.

Fafaroma Francis ya wallafa wani saƙo na ƙin jinin yaƙi a shafinsa na Twitter a harshen Ukraine da Rashanci da kuma Ingilishi, yana mai cewa duk wani yaƙi na mayar da duniya baya fiye da yadda ya same ta”.

“Yaƙi gazawa ce ta siyasa da kuma ɗan Adam,” a cewarsa, yana mai kwatanta shi da “abin kunya, abin alfahari ga miyagu”

Labarai Makamanta

Leave a Reply