Matsalar Tsaro: Za Mu Sayo Jiragen Yaki Daga Turkiyya – El Rufa’i

Mai girma Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El Rufa’i ya ce shi da wasu gwamnoni suna shirin sayo jirage marasa matuka daga Turkiyya domin magance matsalar ‘yan bindiga da ta addabi yankin.

Ya kara da cewa matsalar hare-haren ‘yan fashin daji na dada kamari a shiyyar kuma kasar ba ta da isassun jami’an tsaron da ke iya magance ta.

Hakan ne ya sa, a cewarsa shi da wasu gwamnonin jihohi biyar na Arewa suka yanke shawarar shigowa da jirage marasa matuka wadanda ake dora musu makamai da ake iya sarrafawa daga nesa daga kasar domin taimaka wa sojojin saman Najeriya wajen murkushe su.

El Rufa’i ya bayyana hakan ne a zantawarshi da gidan rediyon BBC.

Related posts

Leave a Comment