Tsaro: Kungiyar Matasan Arewa Ta Yi Kiran Buhari Ya Kori Monguno

Kungiyar Matasan Arewacin Najeriya ta yi kira da babban murya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi hanzarin sallamar mai bashi shawara akan harkar tsaro Janar Monguno wanda shine me ba shugaban ƙasa shawara da akayi wanda yafi kowanne rashin tabuka komai a tsawon shekarun dimokuraɗiyya.

A gida a ba tsira ba, a hanya haka, a gonaki, da duka wuraren neman abinci, biyan fansa ya zama kaman ba komai ba, shi saboda yana inda tsaro yake, yasan yan ta’adda basu iya kaiwa gareshi, shi yasa yake yadda ya ga dama, ya na office, yana samun kudade, su kuma yan Nijeriya anata kashesu ba dare ba rana. Subhanallah. Allah ka tsare mu.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mai magana da yawun kungiyar Matasan na Arewa Aliyu Muhammad a yayin wata ganawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Matasan sun koka akan halin shugaban ƙasa, na nuna halin ko in kula daga bangarenshi, talakawa da suka zabe shi, suka tsaya kai da fata, sukace sai an kawo canji, Allah ya yarda canji yazo, amma kuma gashi ya bari anata kashe su. Kuma daga cikin dalilan zabensa akwai tsaro, saboda ana sa rai zai in ganta tsaro, amma gashi yau kuma, tsaro ya lalace, saboda ya dauko Janar Babagana Mungono mai ritaya wanda ya gaza taɓuka komai, har ya kai wasu na cin zarafin Buhari.

“A bisa wannan dalilan yasa muka shirya zanga zanga ta lumana da zamu gabatar ranar laraba mai zuwa a fadar shugaban kasa domin mu nuna bacin ran mu, da kuma rashin yardar mu akan kashe kashen da aketayi a Nijeriya, domin dolene a tsaya ayi gyara don inganta Nijeriya”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply