Shugabancin Najeriya Ya Fi Karfin Yaro – Tinubu

Rahotannin dake shigo mana daga Ibadan babban birnin Jihar Oyo na bayyana cewar tsohon gwamnan Jihar Legas kuma jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya faɗawa matasan ƙasar cewa za su yi shugabancin ƙasa amma sai bayan ya yi.

Fitaccen ɗan siyasar ya faɗi haka ne a ziyarar da ya kai wa Alaafin na Oyo Lamidi Adeyemi, a ranar Lahadi.

Tinubu ya buƙaci matasa su ba magabatansu dama.

“Kun toshe wa magabatanku dama tun kafin ku zama shugaban ƙasa, idan kun zama shugaban ƙasa fa, za ku kore mu ne a gari?”

“Sai kun tsufa za ku zama shugaban ƙasa, kuma sai na riga zama shugaban ƙasa,” in ji Tinubu.

Matasa a Najeriya sun daɗe suna fafutikar ganin sun kai ga madafan iko, da samun muƙaman siyasa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply