Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC mai mulkin ta saka ranar 26 ga watan Maris don gudanar da babban taronta na ƙasa.
Rahotanni sun bayyana cewa mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Salisu Na’inna Dambatta, ya shaida hakan ga manema labarai za a gudanar da taron ne a Abuja.
Jam’iyyar ta cimma matsayar ne jim kaɗan bayan ta sanar da fasa gudanar da taron wanda a baya aka shirya gudanarwa a ranar 26 ga Fabarairu.
Rahotanni sun bayyana cewa mambobin kwamitin riƙo na shugabancin APC ƙarƙashin Gwamna Mai Mala Buni sun yi wata ganawar sirri a ranar jiya Litinin.
Tun farko dai jam’iyyar APC ta sanar da hukumar zaɓe ta INEC cewa za ta gudanar da tarukan shiyya kafin na ƙasa baki ɗaya.