Shugabancin Kasa: Tsohon Dogarin Abacha Ya Bi Sahu

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon babban dogarin shugaban ƙasa na mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha, wato Manjo Hamza Al-mustapha ya bayyana aniyar sa ta ɗarewa karagar mulkin kasar a shekarar 2023.

Al-Mustapha ya ce idan har ya zama shugaban kasar, a cikin wata shida zai kawo karshen matsalar tsaro ta Boko Haram da ta addabi Najeriya.

Almustapha ya ce, zai je ya tare a dajin Sambisa, da ke jihar Borno, inda nan ne ake ganin matattarar mayakan Boko Haram, tsawon sati daya domin daukar duk matakin da ya wajaba a dauka domin ganin karshen mayakan.

Ya nuna takaicinsa da damuwa kan yadda yake ganin sojojin Najeriya yanzu sun lalace ba su da kishi da kuzari kamar da, inda ya ce, ”Ka ga soja, duk sojan Najeriya ni ina ganinsa daidai yake da dan-sanda na da, saboda sun riga sun zama dan-sandan, kuma ‘yan-sandan da kuke da su sun gurbata, sun gurbata.

Ya ce zai yi wa sojojin Najeriya garambawul a cikin wannan wa’adi na wata shida, wanda hakan abu ne da zai kasance da zafi amma kuma ya zama wajibi domin ya dawo da karfi da kuzarin sojojin Najeriya kamar yadda aka san su a baya.

Tsohon dogarin na Abacha yana magana ne a hira ta musamman da BBC, inda ya bayyana shigarsa jerin masu neman takarar shugabancin kasar a zaben da za a yi a shekara mai zuwa ta 2003, inda zai nemi takara a karkashin jam’iyyar Action Alliance.

Haka kuma ya nuna sakacin gwmnatin Buhari na yadda, ya ce idan Shugaban ya danka wa mutane amana ba ya bibiya, inda ya ce shi idan ya samu shugabancin daga kansa zai nuna misali na bin doka, kuma idan ya dauki rantsuwa to ba zai sassautawa kowa ba, domin doka kamar ruwan zafi take, duk wanda ya saba doka, to doka za ta hau kansa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply