Shugaban Kasa Ya Tafi Hutu Birnin Daura

A yau Juma’a 11 ga watan Disamba Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi gida Birnin Daura ta jihar Katsina domin kai ziyara, da samun hutu da ganawa da ‘yan uwa da abokanan arziƙi da sauran jama’a masoya.

Kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya sanar da cewa jirgin shugaban kasar mai saukar ungulu ya sauka a Katsina a ranar Juma’a don ziyarar mako daya.

Jirgin da ke dauke da shugaban kasar ya dira a filin tashi da saukan jirage na Musa Umaru Yaradua da ke Katsina misalin karfe 4.45 na yammacin ranar Juma’a inda gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina da mataimakinsa da wasu shugabannin hukumomi suka tarbe shi.

Har wa yau cikin tawagar da ta tarbi shugaban kasar akwai mai marataba sarkin Daura Alhaji Umar Faruk Umar da sauran ‘yan majalisun masarautar jihar tare da kayatattun dawakai da fadawa, jim kadan da saukarsa, Sarkin Daura ya ba shugaban kasa kyuatar doki da takobi da aka kawata shi a matsayinsa na Bayajiddan Daura.

Yayin da ya ke Daura, shugaban kasar zai gana da mutane daban daban da suka shafi ‘yan uwa da sauran na kusa da shi amma zai halarci taron Majalisar zartawa a ranar Laraba ta fasahar bidiyo da sauti na intanet wadda mataimakinsa Yemi Osinbajo zai jagoranta.

Rabon shugaba Buhari da zuwa Daura tun watan Disambar bara saboda dalilan annobar korona da ta takaita zirga-zirga a kasashen duniya ciki har da Najeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply