Bauchi: Gwamna Ya Nemi A Sake Duba Dokar Hukuncin Cin Zarafin Mata

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Abdulladir Mohammed ya bukaci a sake duba yanayin dokan cin zarafin mata, domin basu damar sauke nauyin da Allah ya dora masu, don a tabbatar da hukunta masu aikata cin zarafin mata da sauran laifuffuka.

Gwamnan yayi wan nan furucin ne a lokacin da Uwar Gidan Gwamnan Jihar Hajiya Aisha Bala Mohammed, inda suka kai masa ziyarar tuntuba kan ranaku 16 na rajin kare hakkinsu, tare da dumbin mata a gidan gwamnati.

Gwamna Bala yace, lokaci yayi da gwamnatin tarayya zata tanbatar da kawu karshen rashin tsaro da yayi kamari a jihohin arewacin kasan nan, musamman arewa maso gabas da kuma arewa maso yamma.

Kana yace, ya bada umurni ma babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan Shari’a na jiha da kwamishinan Yan’sanda na Jihar Bauchi da su tabbatar da bada hukunci mai tsananin gaske kan masu aikata wan nan mummunan ta’asa ga yaya mata dama yara kanana.

Bala ya kara da cewa wan nan dokan da suka sa hannun na cin zarafin mata, alamace ta gwamnatin jihar kan samu mafita ga wan nan masha’a damn marasa imani suke aikatawa a cikin alumma.

Anata tsokacin Uwar Gidan Gwamnan, Hajiya Aisha Bala ta jinjina ma kokarin gwamnan ta wajen jajircewa da taimaka ma mata da yara, kan wan nan babbar matsalar, tace babu shakka abun a yaba ne.

Aisha Bala ta kara da cewa kimanin mata da yara su miliyan 234 ne wadan da yan uwansu na jikin su ne ke cin zarafinsu a shekaru da dama da suka shude, tace kasa da Kashi ar’ba in ne na matan da ake cin zarafinsu suke fadi ko kuma suke naman taimako wurin al’umma.

Matar gwamnan ta sake cewa ofishinta tare da maaikatar mata da chi gaban kana nan yara ta jihar zasu tabbatar da sun kawo karshen cin zarafin mata ko wani iri ne a dukkanin fadin Jihar.

A jawabin ta na maraba kwamishinan mata da yara kana nan Hajiya Hajara Gidado, itama ta yaba da hobbasan uwar gidan gwamnan da tallafa ma mata da marasa galihu.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta

Leave a Reply