Rundunar Soji Ta Shiga Farautar Makasan Janar Hassan Ahmad

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumomin tsaro sun fara bincike kan kisan wani Janar din soja, Hassan Ahmed, wanda wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka harbe a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja.

An ruwaito cewa sojojin na Najeriya da sauran hukumomin tsaro sun kaddamar da wani mummunan farmaki na hadin gwiwa a yankin Koton Karfe na Jihar Kogi, inda aka kai wa jami’in sojin hari.

‘Yar uwarsa wacce take cikin motar tare da shi, rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da ita yayin da direbansa ya tsere.

Kwanan nan, hanyar Koton Karfe ta kasance matattarar ‘yan fashi da makami, wadanda yawanci sukan addabi masu ababen hawa.

Baya ga yawan sace-sacen mutane, ‘yan fashin suna karbar kudin fansa ga mutanen da suka sace a garuruwansu. An ruwaito cewa marigayin Janar din shi ne tsohon mai mukamin Provost Marshall na rundunar sojojin Najeriya.

An yi jana’izarsa a Abuja An binne Janar Ahmed ne a ranar Juma’a, 16 ga Yuli, cikin yanayi na girmamawa irinta soja da yabo a makabartar Barikin Lungi da ke Abuja, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. Kakakin rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya ce rundunar ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mamacin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply