Buhari Na Nuna Kabilanci Wajen Rabon Arzikin Kasa – Gwamnan Binuwai

Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya ce kololuwar yaudara da munafurci ne ya sa Gwamnatin Tarayya ta amince da Naira biliyan 6.25 don kiwon zamani a Jihar Katsina har ta riga ta saki Naira biliyan 5, yayin da ita gwamnatin ke neman dawo da burtalolin shanu da zimmar karfafa kiwo a fili a wasu jihohin na tarayya.

Gwamna Ortom, wanda ya fadi hakan a filin jirgin saman Makurdi, yana mayar da martani ne ga bayanan da Gwamna Bello Masari ya yi, yayin kaddamar da aikin Madatsar Ruwa ta Zobe a Dutsinma da ke Jihar Katsina.

Zaku tuna cewa Masari yace shugaban Kasa ya amince da N6.25b domin aikin habaka kiwon zamani a Jihar Katsina, daga cikin kudaden, N5b na cikin asusun gwamnatin jihar.

Gwamna Ortom ya kafe kan cewa ya kamata Gwamnatin Tarayya ta nemi gafarar sa tare da bada irin wannan karimcin ga Jihar Benuwai ta hanyar tura N100b ga jihar domin kafa wuraren kiwon zamani a jihar.

“Don haka, Maigirma Shugaban Kasa ya amince da N6.5b domin kiwon zamani a Jihar Katsina. Wannan wane irin munafurci ne? Shin muna da kasa mai ma’ana kuwa?

“Idan Shugaban Kasa zai ce Babban Lauyan Tarayya ya tabbatar da sake tashin wadanda suka keta haddin burtalolin shanu da wuraren kiwo domin dawo da yin kiwon sake duk da karuwar da jama’a suka yi daga kasa da miliyan 40 a shekarar 1950 zuwa sama da mutum miliyan 200 a yau.

“Kuma wannan Shugaban yana karfafa gwiwar kiwo a Jihar Katsina inda ya fito, wannan tabbas abin dariya ne da munafurci da yaudara. “Don haka idan Shugaban Kasar ya amince da N6.5b ga Jihar Katsina, to lallai ne gwamnatin ta amince da ware N100b ga Jihar Binuwai tare da neman afuwa a gare ni.

Gwamna Ortom ya kara da cewa ba daidai ba ne ga Gwamnatin Tarayya ta amince da kudi don kiwo a cikin wata jiha ta bar wasu jihohin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply