Gwamnatin Nijeriya ta bayar da kudaden da yawansu ya kai kimanin Naira biliyan uku domin gina kashin farko na gidaje dubu 10 da za a sake mayar da ?an gudun hijira a jihar Borno.
Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a ziyarar gani da ido da ya kai a sashen da za a gina sabbin gidajen a garin Dalori da ke karamar hukumar Konduga.
Zulum ya ce gwamnatin ta bayar da kudaden ne ga jihar domin tabbatar da aiwatar da wannan muhimmin aiki domin ?an gudun Hijirar su dawo gida su ci gaba da rayuwarsu kamar yadda suka saba.
Ku cigaba da kasancewa damu a shafin mu na www.muryaryanci.com domin samun ingantattun labarai da ruhotanni da dumi dumin su