Najeriya Na Matsayi Na Takwas A Ayyukan Ta’addanci A Duniya

A cewar rahoton bincike da ake yi gameda ayyukan ta’addanci da aka fitar a wannan shekarar, ya nuna cewar ayyukan ta’addanci a karon farko sun ragu sosai a kasar tun bayan shekarar 2011.

Daga tsakanin shekarar 2017 zuwa 2020, Najeriya na mataki na hudu a jerin kasashen da aka fi samun ta’addanci a duniya, duk da cewa lamarin ya fi kamari a shekarar 2016 da 2015 da kasar ke a mataki na 2.

Kungiyoyin masu ta da kayar baya irin su Boko Haram da kuma ISWAP sun yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane a shiyar Arewa maso Gabashin kasar, a hare-haren da suke kaiwa.

A cewar rahoton, a shekarar 2021 mutane 497 suka mutu sanadiyar ayyukan ta’addanci inda kuma adadin ya ragu zuwa 385 a shekarar da ta gabata.

Haka nan kuma, adadin hare-haren ta’addancin da aka kai a shakarar 2021 ya ragu zuwa 214 sannan a shekarar da ta gabata ya kara yin kasa zuwa 120, wanda shine karo na farko da aka samu irin wannan raguwa tun shekarar 2011.

Labarai Makamanta

Leave a Reply