Kaduna: An Harbe ‘Yan Shi’a 6 A Yayin Artabu Da Tawagar Gwamna

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar a yammacin ranar jiya Alhamis ne ƴan SHI’A mabiya Zakzaky suka fito kan titi domin kira ga gwamnati aka a sakar wa malaminsu fasfo ɗinsa na fita kasar waje domin neman magani.

Ƴan shi’ar dai sun fito suna faɗin Free Zakzaky fasfo a daidai lokacin da tawagar Gwamnan jihar Nasiru El-Rufa’i ta zo wucewa ta wurin a yankin titin Byepass, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, lamarin da ya haifar da artabu tsakanin su da tawagar Gwamnan tsaro suka iso wajen su suna harba musu tiyagas ganin haka yasa mabiya shi’ar suka dinga faɗin Allahu Akbar daganan sai jami’an tsaron suka fara harbinsu da bindiga harsashi mai sai haka yai sanadiyar rasuwar mutane shida a cikin ƴan shi’ar tare da raunata wasu da dama.

Ga sunayen waɗanda aka kashe a wajen.
(1) Aliyu Sulaiman
(2) Abubakar Nura(Abba)
(3) Ibrahim Abdullahi (Cash money)
(4) Yasir Isma’il Abduzzahara
(5) Abdulmalik Ibrahim (Yawale)

Labarai Makamanta

Leave a Reply