Mai Shadda Zai Angwance Da Jaruma Hassana Muhammad

Furodusa a masana’antar Kannywood da ke arewacin Najeriya Bashir Abdulkareem Mai Shadda, zai angwance da amaryarsa jaruma Hassana Muhammad.

Za a daura auren ne a unguwar Masallacin Murtala da ke Kano a ranar 13 ga watan Maris kamar yadda Maishadda ya sanar.

“Ina farin cikin gayyatar masoya daurin aurena. Wadanda kuma ba za su samu damar zuwa ba, sai a taya mu da addu’a.” Mai Shadda ya rubuta a shafinsa na Instagram hade da katin gayyata a ranar Talata.

Jaruma Hassana Muhammadu na daya daga cikin jaruman Kanyywood mata da tauraronsu ya haska musamman a shekarar 2020.

Ta fito a manyan fina-finai irinsu “Hafiz” da “Hauwa Kulu,” tare da Umar M. Shareef, wadanda duk kamfanin Maishadda Global Resources ne ya shirya.

Kazalika ta fito a fim din Mujadala da aka sabunta. Sai dai an dena jin duriyarta a baya-bayan nan a fina-finan na Kannywood.

Labarai Makamanta

Leave a Reply