Kaduna: ‘Yan Bindiga Na Neman Miliyan 100 A Hannun Jami’in DSS Da Suka Sace

Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun sace jami’in ne tare da dansa mai shekaru hudu a hanyar Rigachikun zuwa Afaka a ta jihar Kaduna.

Jami’in da har yanzu ba a bayyana sunansa ba ya fada hannun masu garkuwar ne a hanyar Rigachikun zuwa Afaka a ranar Litinin kamar yadda majiyarmu ta ruwaito.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun tuntubi iyalansa sun nemi a biya su kudin fansa Naira miliyan 100 kafin su sako shi.

Jami’in da aka yi garkuwa da shi yana aiki ne a matsayin mai kula da inda ake ajiye makamai na makarantar horas da sabbin jami’an DSS.

Hakan na zuwa ne awanni kadan bayan ‘yan bindiga sun kashe wani jami’in DSS mai shekaru 33 mai suna Sadiq Abdullahi Bindawa duk da kudin fansa Naira miliyan 5 da aka biya.

Marigayi Bindawa yana gidansa ne da ke bayan sakatariyar gwamnatin tarayya a Katsina yayin da ‘yan bindigan suka kai masa hari. Bindawa yana aiki ne da sashin tattara bayannan sirri na hukumar da ke Abuja.

Labarai Makamanta

Leave a Reply