Kungiyar OPC Ta Yi Tir Da Ziyarar Gumi Kasar Yarbawa

Kungiyar Yarabawa ta Oodua Peoples Congress, OPC, reshen jihar Oyo karkashin jagorancin Aare Onakakanfo na kasar Yarbawa, Gani Adams ta ce ziyarar da Gumi ya kai ta bazata jihar Oyo cin fuska ne ga Yarbawa baki daya.

A yayin zantawarsa da manema labarai a karshen mako, Rotimi Olumo, jagorar OPC a jihar Oyo ya ce Gumi yana wuce gona da iri kuma ya gargade shi ya kiyayi yankin Kudu maso Yamma na kasar Yarbawa.

A cewar Olumo, ziyarar Gumi babban barazana ce ta tsaro ga dukkan yankin Yarbawa domi ba su ga amfanin hakan ba sai dai cin fuska da kokarin wofintar da mutanen kudu maso yamma. Ya ce sukar da Gumi da tawagarsa ke yi wa Igoho alama ce da ke nuna sun zo wurin ne domin tsokanar fada da cin fuskar Yarbawa a kasarsu, wadda OPC ba za ta amince da hakan ba.

OPC ta yi kira ga mutanen yankin kudu maso yamma su cigaba da sa ido domin Gumi ba abin yarda bane. OPC ta ce ziyarar Gumi zuwa yankin kudu maso yamma lamari ne mai alamar tambaya, domin ana zargin ya zo ne a matsayin dan leken asiri na ‘yan bindiga.

Olumo ya ce shugabannnin OPC na jihar Oyo sun gamsu da jagorancin Iba Gani Adams kan yadda ya ke gudanar da ofishin Aare Onakakanfo na kasar Yoruba da batun tsaro baki daya. Ya kuma yaba wa gwamnonin yankin kudu maso yamma bisa kokarinsu na ganin an samu zaman lafiya a yankin, yana mai cewa mutanen yankin a shirye suke su bada hadin kai ga jami’an tsaro don kiyayye rayuka da dukiyoyin al’umma.

Labarai Makamanta

Leave a Reply