Borno: Zulum Ya Dauki Nauyin Iyalan Shugaban ‘Yan Sa Kai Da Aka Kashe

Rahotannin daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana Gwamna Babagana Zulum na Jihar ya bada kyautar gida da Naira miliyan 10 ga iyalan tsohon kwamandan yan sa kai na civilian JTF, Babagana Tela, wanda Boko Haram suka kashe.

Mista Tela wanda aka fi sani da ‘Kadau’ saboda jarumtarsa shine kwamandan JTF a Bama, daya daga cikin garuruwan da aka kwato a Borno daga hannun mayaƙan Boko Haram.

Sanarwar da Isa Gusau, mashawarcin Gwamna Zulum a bangaren watsa labarai ya fitar ta ce gwamnan wanda ya ziyarci iyalan mamacin ya kuma amince gwamnati ta dauki nauyin karatun yaransa. “Gwamna ya bada umurnin a bada N10m don kula da iyalan mamacin na wani lokaci, ya bukaci su bude asusun baki na hadin gwiwa inda za a saka kudin.

“Zulum ya kuma umurci a fitar da Naira miliyan 10 a siya wa iyalan Kadau gida saboda su daina biyan kudin haya. “Zulum ya kara da cewa gwamnatin jiha za ta dauki nauyin karatun yayan marigayin har su kammala.

Labarai Makamanta

Leave a Reply