Kimanin ‘Yan Najeriya 76,000 Ne Aka Kashe Cikin Shekaru Goma – Gwamnonin Najeriya

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta ce daga tsakanin watan Mayun 2011 zuwa Fabirairun 2021, an kashe sama da mutum 76,000 a kasar kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Shugaban kungiyar kuma Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi ne ya bayyana hakan a Abuja a jiya Alhamis, yayin da kungiyar ta kaddamar da wani shirinta na samar da zaman lafiya da tsaro.

“Bugu da kari kan bazuwar makamai a cikin jama’a da kuma karuwar rikicin kabilanci, yayin da kabilu da yawa da kungiyoyinsu ke ci gaba da hamayya da juna,” in ji shi.

Fayemi ya kara nuna damuwa kan yaddda rashin tsaro ke kara rugurguza zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Ya ce halin da tsaro ke ciki ya zama barazanar da ta sa duk dan Najeriya baya iya gano haske a goben kasar.

Gwamnan ya ce matsalar tsaro da karuwar muggan ayyuka na kara haifar da koma baya ga gwamnati da kuma janyo rashin yarda tsakanin mutane.

Labarai Makamanta

Leave a Reply