Kungiyar Kare Hakkin Mata Ta Maka Buhari Kotu

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gamayyar kungiyoyin mata sun shigar da karar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a gaban wata kotun tarayya dake Abuja.

Kungiyoyin su na ikirarin cewa gwamnatin da Muhammadu Buhari yake jagoranta, ba ta yi da mata. A wannan kara da kungiyoyin suka shigar, sun bukaci kotu ta hana shugaban Najeriyar cigaba da saba ka’idar da ta ce a ba mata kashi 35% na mukaman gwamnati.

Wadannan kungiyoyi na mata sun ce kin ba mata akalla 35% na kujerun gwamnatin tarayya ya saba kundin tsarin mulki da ka’idar jinsi na shekarar 2006.

Kungiyoyin sun ce ware su da aka yi, ya saba wa tsarin kare hakkin Bil Adama na Afrika. Har ila yau wadannan masu kare hakkin mata sun zargi gwamnatin tarayya da watsi da dokar kasa wajen ke ba mata mukamai da kuma kujeru masu tsoka.

An shigar da kara a kotu, an soma shari’a Marshal Abubakar shi ne lauyan da ya shigar da wannan kara a gaban Alkali Donatus Okorowo. Ibukun Okoosi shi ne lauyan da ya ke kare wadanda ake tuhuma.

Labarai Makamanta

Leave a Reply