Kano: Hatsarin Kwale-Kwale Ya Ci Rayukan Daliban Islamiyya


Rahotannin dake shigo mana daga daga jihar Kano na bayyana cewar mutane da dama ciki har da daliban Islamiyya ne suka mutu sakamakon wani mummunan hatsarin kwale-kwale daya wakana a karamar hukumar Bagwai.

Rahotannin sun nuna cewa fiye da mutum 30 ne suka bata bayan hatsarin kwale-kwalen da yammacin ranar Talata.

Bayanai sun nuna cewa mutanen sun taso ne daga kauyen Badau zuwa garin Bagwai domin yin maulidi amma kwale-kwalen ya nutse da su.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa kwale-kwalen yana dauke da mutum kusan 50.

Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa wakilinmu cewa “kwale-kwalen mai dauke da kusan mutum hamsin ya kife a kogin Bagwai.

“Ya zuwa yanzu mun gano gawar mutum ashirin, sai kuma mutum bakwai da aka ciro da ransu sanna ana ci gaba da neman wasu da dama da suka nutse.”

Ganau sun shaida mana cewa jirgin ya nutse ne a kogin Bagwai sakamakon daukar mutane fiye da kima.

Labarai Makamanta

Leave a Reply