Birtaniya Ta Sha Alwashin Taimakawa Najeriya Shawo Kan Matsalar Tsaro

Rahotanni daga birnin London na Kasar Ingila na bayyana cewar Firaiministan Burtaniya Boris Johnson ya ce kasarsa a shirye ta ke ta taimaka wa Najeriya kan matsalar tsaro da ke damunta.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaba Buhari, Femi Adesina ya fitar ta ce, Boris Johnson ya bai wa shugaba Buhari wannan tabbaci ne a gefen taron habbaka ilimi da ke gudana a Landan.

Bayan duban tsanaki da shugabannin suka yi wa matsalar tsaron kasar, sun amince da cewa dole a kyale bangaren shari’a ya yi aikinsa yadda ya kamata.

Duka shugaban sun yarda cewa dole a kyale shari’a ta rika aikinta ba tare da katsa-landan ba, kuma ko da wanene shari’ar ta shafa.

Buhari ya kuma yi wa Firaiministan bayani a takaice kan ikon da Najeriya ke bukatar samu da kuma kokarin da take yi na tabbatar da ta samar da abincin da za ta iya rike kanta da shi.

Ya kuma yi masa bayanin matsalar tsaron da yankunan Najeriya ke ciki.

A nasa bangaren Johnson ya bayyana cewa a shirye suke su taimaka a kawo karshen wannan rikici.

Labarai Makamanta

Leave a Reply