Kano: Ban Da Abokin Gaba A Siyasa – Ganduje

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana a kan sabaninsa da bangaren Malam Ibrahim Shekarau a rikicinsu na cikin gidan APC.

Da aka yi hira da shi a Gidan Rediyon RFI Hausa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa sam ba wani abin mamaki ba ne don an samu rashin jituwa a siyasa. A cewar Dr. Abdullahi Ganduje, uwar jam’iyya ta na kan kokarin sasanta wannan rikicin cikin gidan.

“Ana nan ana sasantawa, kamar yadda ka sani, uwar jam’iyyar ta shiga. Kuma samun rabuwar kai a siyasa ba sabon abu ba ne, a daidaita ba sabon abu ba ne.” “Saboda haka duka masu wannan, da dukkanmu ‘yan siyasa ne, mun san wani lokaci za a bata, wani lokacin kuma sai a shirya.”

Abdullahi Ganduje yace ba yau ya fara siyasa ba, gwamnan yace ya dade a wannan harka. “Amma abin da muke cewa shi ne, wannan siyasa ba wai mun tsince ta a bakin titi ba ne. Mun shige ta ne fiye da shekara 40 da suka shige.”

“Kuma bugu da kari ma, ita mu ka karanta a jami’a, kuma ita mu ke yi. Saboda haka mun san siyasa harka ce ta hakuri.”

“Ba a yin abokin gaba na din-din a siyasa, sai dai ma abokin din-din-din saboda yadda mutane suke canza alkibla. A karshe Abdullahi Ganduje yace ya na sa ran hakarsu za ta cin ma ruwa wajen sasanta ‘yan APC.

Labarai Makamanta

Leave a Reply