Jiragen Yakin Soji Sun Yi Ruwan Bama-Bamai Kan ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar wani ruwan bama-bamai da jirgin yakin rundunar Operation Hadarin Daji ya yi, ya hallaka adadi mai yawa na yan bindiga a yankin arewa ta yamma.

A rahoton PRNigeria, harin jirgin yakin, wanda sojojin sama suka aiwatar a Dangwandi da Tsakai dake karamar hukumar Isa, ya yi sanadin mutuwar ƙusoshin yan bindiga da dama.

Kazalika makamancin irin wannan ruwan bama-baman ta sama, ya hallaka kayayyakin amfani yan bindiga da yawan gaske a wasu sassan Zamfara.

Labarai Makamanta

Leave a Reply