Ina Samun Dubban Kudade A Hannun ‘Yan Bindiga A Kullum – Dillalin Biredi

Jami’an ‘yan sanda karkashin sashin binciken manyan laifuka na IRT tayi nasarar kama masu kaima yan ta’adda burodi a_ sansaninu dake Jihar Kaduna.

Hassan Magaji Wanda Yana daya daga cikin wanda ake zargi mamalakin Gidan Burodi ne, Kuma ya fi samun riban siyarwa yan fashi akan saidawa sauran mutane. Akwai hatsari a tattare da kaima yan fashi burodi dan ana iya kame a kowani lokaci Hukumar yan sanda ta cika hannu da masu kaiwa yan bindiga Burodi ranar 8 ga Yuni yayinda suka nufi shiga dajin Damari, yankin karamar hukumar Birnin Gwari.

Wadanda ake zargin su ne Hassan Magaji, Abubakar Ibrahim, Auwal Abubakar da Ibrahim Kabiru an kamasu ne a ranar 8 ga watan Yuni da misalin karfe 5 na yamma yayin da suke kan hanyar su na zuwa Dajin Damari don kai biredin da ake zargin na ’yan fashi ne. Jaridar Saturday Sun ta labarin cewa jami’in ya sun yi aiki ne bisa bayanan sirri da suka samu cewa, wadanda ake zargin suna kai kayan abinci tare da kai rahoton bayanai ga ‘yan ta’addan a sansanonin Galadimawa, Damari, Kidandan da na Awala duk a kan iyakar Birnin Gwari da karamar hukumar Giwa a Kaduna. Wadanda ake zargi sun kai ‘yan sanda masana’antar inda aka gano burodi kimanin guda 150.

Mamallakin Gidan Biredin, Hassan Magaji a wata hira da aka yi da shi ya shaidawa Jaridar Saturday Sun cewa ya fara kai wa ‘yan fashin burodi ne lokacin da ya fahimci cewa ita ce hanya mafi sauki da zai sayar da kayayyakinsa a kan farashi mafi tsada.

Inda yace: “Ni shekaru na 29 kuma haifaffen ƙauyen Galadimawa da ke Jihar Kaduna. Na yi aure da mata biyu Allah ya albarkace ni da yara uku. Da babur nake ja ina kasuwanci amma sai na fahimci abun babu riba saboda masu sata. Sun sha kwacemin babur. “Kwatsam wani dan uwana, Mustafa Magaji wanda ke da gidajen burodi da dama, ya kawo min ziyara a shekarar 2018 inda ya koya min yadda ake gasa biredin. Nayi amfani da N21, 000 wanda na yi kokari na tara domin fara kasuwancin kuma a yanzu ina samun akalla N400, 000 a wata. Bunkasar kasuwanci na ya fara ne lokacin da na fara samar da burodi ga ‘yan ta’adda.

Labarai Makamanta

Leave a Reply