Farfado Da Darajar Naira: Tinubu Ya Gwada Kwarewa A Mulkin Najeriya – Kashim Shettima

Kashim Shettima office portrait

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa mataimakin shugaban kasa Alhaji Kashim Shettima ya bayyana cewa shugaban kasa Tinubu ya yi rawar gani wajen sake dawo da martabar Naira wadda a baya ta durkushe.

Mataimakin Shugaban Ƙasar, Shettima, wanda ya faɗi hakan ranar Juma’a lokacin da tawagar Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Legas (LCCI) ta kai masa ziyara a ofishinsa da ke Abuja, ya ce sun san ƙalubalen da ake fuskanta amma duk da haka suka zagaye ƙasar suna neman a zaɓe su saboda sun san cewa Bola Tinubu zai iya magance matsalolin.

“A baya wasu sun rinƙa farin ciki bisa ga karyewar darajar Naira, yayin da a hannu guda mu kuma muke yi musu dariya saboda sanin da muke dashi na kwarewar shugabancin Tinubu zai dawo da komai daidai”

Labarai Makamanta

Leave a Reply