Tsaro Ya Inganta A Mulkin Tinubu – Akpabio

images 2024 03 08T074139.678

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro ta ragu matuƙa a ƙasar nan tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023. Akpabio ya bayyana haka ne a lokacin da yake bayar da gudummuwa a yayin muhawara kan ƙudirin da ya shafi kashe-kashen da aka yi a jihar Benuwai.

A kalamansa: “Aiki na farko da ke kan gwamnatin jiha shi ne ta yi amfani da kuɗaɗen tsaro wajen ganin an kare tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar Benuwai.”

“Tsarin farko shi ne gwamnatin Benuwai, kamar yadda Sanata Udende ya nuna, ba mu ji wani abu daga gare ta ba.” “Idan an kashe mutum 50 aka kuma kai wa al’umma hari, za mu yi tsammanin gwamnatin jihar za ta shirya tsare-tsare tare da jami’an tsaron da ke a jihar da abin ya shafa, su ga abin da za su iya yi kafin a kawo wa shugaban ƙasa Bola Tinubu.”

Ina so na tabbatar maku cewa Shugaba Tinubu, duk da cewa bai daɗe da zama a ofis ba, yana goyon bayan ayyukan rundunar soji.” “A gaskiya tun da ya hau kan karagar mulki, rashin tsaro ya ragu, kuma ba a sake kai manyan hare-hare ba, amma wannan lamarin koma baya ne kawai, kuma za a kawo ƙarshensa.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply