Dokar Zabe: Kotu Ta Bada Umarnin Aiki Da Bukatar Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wata babbar kotun tarayya da ke zama a Umuahia, babban birnin jihar Abia a ranar Juma’a, ta umurci ministan shari’a, Abubakar Malami, da ya shafe sashe na 84 (12) na sabuwar dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima.

Umarnin kotun ya biyo bayan bukatar da shugaban Buhari ya mika wa majalisar dokokin kasar na a soke wani bangare na dokar da ta haramta wa masu rike da muƙaman siyasa tsayawa takara ba tare da yin murabus ba.

A hukuncin da ta yanke, babbar kotun ta bayyana cewa ana bukatar masu rike da mukaman siyasa su yi murabus daga mukamansu ne kawai kwanaki 30 kafin zabe ba da wuri ba kamar yadda sashe na 84(12) na dokar zabe ya tanada.

Da take warware sashen, kotun ta ce ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa saboda ya saba wa tanadin sashe na 66 , 107 , 137 da 182 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 da ya tanadi murabus akalla kwanaki 30 gabanin zabe.

A hukuncin da ta yanke ta ce duk wani tanadi na wata doka da ta saba da sharuddan kundin tsarin mulkin kasar, to ba shi da tushe balle makama. Ya kara da cewa majalisar ta wuce gona da iri ta hanyar amincewa da irin wannan dokar da ta saba wa kundin tsarin mulki wanda shi ne ka’idar kotu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply