Buga Takardun Kudi: Babu Gaskiya A Maganar Obaseki – Ministar Kudi

Gwamnatin Najeriya ta karyata ikirarin da Gwamnan Jihar Edo ya yi cewa ta buga Naira biliyan 60 ta zuba cikin kudaden kasafin da ta ke rabawa a watan Maris.

Ministar harkokin Kudade, Kasafi da Tsare-tsare Zainab Ahmed ce ta karyata Gwamna Obaseki, a lokacin da ta ke wa manema labarai bayani a Fadar Shugaban Kasa.

Minista Zainab ta kara da cewa ikirarin Obaseki abin takaici ne kuma abin haushi, saboda ko kadan ba gaskiya ba ne.

“Wannan ikirari da Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki ya yi ni dai a bangare na, abin takaici ne, abin haushi, saboda ba gaskiya ce ya fada ba.”

Shi dai gwamna Obaseki ya yi magana ce akan matsalar karancin kudaden da kasar nan ke fama da su, inda ya kara da cewa Najeriya na fama da rashin kudi mai tsanani.

Yayin da ya ke magana a taron masu ruwa a tsaki na Jihar, Obaseki ya yi ikirarin cewa sai da Gwamnatin Buhari ta buga kudi har zunzurutun naira biliyyan 60 sannan ta cike wani wawakeken gibi a cikin kudaden da ake raba wa jihohi da kananan hukumomi da kuma ita kan ta gwamnatin tarayya din.

“Sai da Gwamnatin Tarayya ta buga kusan naira biliyan 50 zuwa biliyan 60, sannan aka samu cikon kudaden da ta iya rabawa a kason da aka raba mana a watan Maris.” Inji Obaseki.

To amma Ministar Harkokin Kudede Zainab Ahmed ta shaida cewa kudaden da aka raba a watan Maris, an samo su ne daga kudaden shigar da Gwamnatin Tarayya ta tattaro daga bangarorin samun kudaden shigar kasar nan daban-daban.

“Abin da mu ka raba a cikin watan Maris duk kudaden shiga ne da hukumomun gwmnatintarayya ta tattara daga bangarori daban-daban, musammn Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Kasa (FIRS0), Hukumr Kwastan, NNPC, kuma mu ka raba su ga Gwamnatin Tarayya, Gwamnatocin Jihohi da Kananan Kukumomin kasar nan baki daya.” Inji Zainab.

Da ta ke magana dangane da damuwar da ‘yan Najeriya ke nunawa a kan yawan ciwo bashin da gwamnatin Buhari ke yi bagatatan, Minista Zainab ta ce har yanzu bashi bai kai wa Najeriya har iyar wuya ba, ballantana ya rike mata makoshi ta kasa numfasawa.

Sai dai kuma duk da hakan ta yarda da cewa tabbas akwai bukatar Najeriya ta mike tsaye ta kara inganta hanyoyin samun kudin shigar kasar

Labarai Makamanta

Leave a Reply