Saudiyya Ta Aike Kur’anai Miliyan Guda Ga Kasashe 29

Ma’aikatar kula da harkokin addini ta saudiyya, ta fara raba kur’anai miliyan 1,200,000 fassararru cikin yaruka 21 zuwa kasashe 29 a fadin duniya a matsayin kyauta.

Jirgin wanda ya fara hadin kai tsakanin ofishin jakadancin Saudiyya da ibiyoyin addini da al’ada da kuma Saudiyya a wadancan kasashen.

Da yake magana a lokacin gabatar da taron, Ministan harkokin addinin musulunci Dakta Abdallatif Al Al-Sheik, wanda kuma yake lura da harkokin cibiyar dab’i ta Sarki Fahad, ya yi matukar godiya ga mai yi wa masallatan harami hidima Sarki Salman kan wannan taimako wanda ke nuna yadda yake damuwa ga addinin Musulunci.

Related posts

Leave a Comment