Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Nemi Miliyan 500 Kuɗin Fansar Ɗalibai

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Iyayen daliban kwalejin horar da aikin noma da gandun dabbobi dake yankin ƙaramar Hukumar Igabi Afaka a jihar Kaduna, sun ce an bukaci su biya kudin fansar ‘ya’yansu har naira miliyan 500 kafin a sako su.

An bukaci da su cire rai daga tallafi ko taimakon gwamnati wurin ceto rayukan ‘ya’yansu, duk da 10 daga cikin daliban an sako su kuma tuni suka sadu da iyayensu, sauran suna cikin daji tun a ranar 11 ga watan Maris na 2021.

A yayin tattaunawa da manema labarai a Kaduna a ranar Juma’a, mai magana da yawun iyayen daliban, Friday Sani, ya ce ‘yan bindigan sun fara kiran iyayen domin karbar kudin fansa.

Kamar yadda yace, “Halin da muke ciki a yau na tashin hankali ne kuma muna kira ga duniya da su taimaka mana. Mun yi zanga-zanga kuma gwamnatin jihar Kaduna ta kira mu. Mun yi tunanin zamu ji labari mai dadi amma sai aka sanar damu cewa za a hukunta duk wanda yayi sasanci da ‘yan bindiga.”

“Wannan ne yasa muka sake fitowa a karo na biyu domin sanar da duniya halin da muke ciki duk da an kama mana tunani tare da mallakemu ta yadda aka sace ‘ya’yanmu.

“Tuni dama gwamnati ta kama mu, wasu daga cikinmu basu iya bacci ko cin abinci yayin da wasu suka samu ciwuka, don haka babu kamen da yafi haka,” inji shi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply