Boko Haram: Amfani Da Ƙarfin Soji Ba Zai Biya Buƙata Ba – Zulum

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya bayyana cewar shawo kan matsalar tsaro ta hanyar amfani da dakarun soji a kasar nan ba hanya ce mai bullewa ba ga matsalar tsaro da ta addabi yankin arewa maso gabas.

Zulum ya ƙara da cewar amfani da salon siyasa wurin kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi jihar shine hanya da ta dace, wajen magance matsalar tsaro wadda ta dade ta na addabar yankin.

Farfesa Zulum ya sanar da hakan yayin jawabi ga manema labaran gidan Gwamnati bayan taron sirrin da yayi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Juma’a.

Ya ce yanayin salon da ake amfani da shi a halin yanzu ba zai isa ya kawo karashe matsalar tsaro ba. Gwamnan ya kara da cewa fatara da tsananin talauci ya taka rawar gani wurin assasa matasalar tsaro.

Ya ce dole ne a inganta rayuwar matasa domin gujewa hakan. Ya yi kira ga gwamnati a kowanne mataki da ta samar da ayyukan yi ga matasa tare da samar da muhalli ga jama’ar da suka bar gidajensu na gado domin samun mafaka.

Ya ce mulkinsa ya dage inda ya mayar da a kalla mutum 100,000 da suka samu mafaka bayan mayakan ta’addancin Boko Haram sun fatattakesu.

Gwamnan ya ce komawar jama’a gidajensu na gado alamu ne da ke nuna cewa tabbas zaman lafiya ya dawo yankin Borno.

Labarai Makamanta

Leave a Reply