Shugaban Kwamitin raba dai-dai na majalisar Dattawa mai wakiltar Kudancin Kaduna, Sanata Danjuma La’ah ya karyata labarun da suke yawo a kafafen yada labarai cewa ya nemi a hana shugaban kasa Buhari fita waje neman lafiya.
Sanata La’ah ya ce shi dai ya nemi a Inganta asibitin fadar Shugaban kasa ne domin a rika duba Shugaban Kasa da sauran ma’aikatan Gwamnati, amma mutane suka karkatar da maganar sa zuwa wata manufar.
A kwanakin baya ne dai aka yi ta yama?i?i da maganar da Sanatan ya yi na cewar, a haramtawa Shugaban ?asa da iyalansa fita waje neman magani, ya zamana cewar su tsaya a Asibitocin gida.
Ana hasashen cewa Sanata La’ah ya janye ?udurin nashi ne biyo bayan matsin lamban da ya fuskanta a tsakanin takwarorinshi dake majalisar Dattawa.