Bamu Da Wani Shiri Na Daukar Fansar Kisan Da Jami’an Tsaro Suka Yi Wa Yaranmu – Sheikh Zakzaky

IMG 20240414 WA0032

Kungiyar IMN a Najeriya da aka fi sani da Shi’a ta ƙaryata cewa za ta dauki mataki kan kisan ‘yan ƙungiyar. Shugaban kungiyar, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya ce babu wani shiri na dakar fansa kan abin da ya faru.W

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Isah Hassan Mshelgaro ya fitar a madadin kungiyar ta kasa.

Kungiyar ta ce Sheikh Zakzaky ya kadu da samun sakon da ‘yan sandan ke yadawa kan shirin daukar matakin. “Muna son sanar da al’umma cewa babu wani shiri na daukar fansa kan kisan ‘yan uwanmu guda bakwai da aka yi a jihar Kaduna kan ‘yan sanda ko wata kungiyar ko jama’a.”

“Wannan abin kunya ya fito ne daga hedkwatar ‘yan sanda daga jihar Borno wacce nisanta da jihar Kaduna ya kai kilomita 800.”

Kungiyar ta kara da cewa a shekarun bayan an hallaka mambobinta da dama amma ba ta dauki mataki ba, sai dai kuma hakan ba ya na nufin ba su san me suke ba. Ta ce duk abubuwan da suka faru akwai ranar da adalci zai bayyana amma dai ba za su taba mantawa ko yafewa ba.

 

Labarai Makamanta

Leave a Reply