Babu Hikima A Martanin Da Bello Matawalle Ya Yi Wa Dattawan Arewa – Hakeem Baba Ahmed

IMG 20240415 WA0079

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa tsohon kakakin Kungiyar Dattawan Arewa kuma Mai ba da Shawara a kan Siyasa ga Maitamakin Shugaban Kasa Dokta Hakeem Baba Ahmed a Shafinsa na facebook ran lahadi yace babu hikima ko fahimta a martanin da ƙaramin Ministan tsaro Bello Matawalle ya yi wa Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) bayan ta koka a halin da Arewa take ciki.

“Da ya fadi irin gudunmuwar da ministoci daga Arewa kamar shi, da masu sauran mukamai kamar ni suke bayar wa ne, da kuma fa’idar gudunmuwar, da yafi wa wannan gwamnatin amfani. Shi ya sa shiga sharo ba shanu ba shi da amfani”.

Idan jama’a ba su manta ba a kwanakin baya ne kungiyar Dattawan Arewa ta bakin mai magana da yawunta Abdulaziz Suleman suka koka dangane da halin koma baya da arewa ke ciki a mulkin Tinubu inda suka ce Shugaban ba zai samu goyon bayan yankin ba a shekarar zaɓe ta 2027.

To sai dai da yake mayar da martani akai karamin ministan tsaro Bello Matawalle ya soki lamirin Ƙungiyar Dattawan inda ya bayyana Ƙungiyar a matsayin Jam’iyyar Adawa ta siyasa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply