Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta kama Akanta Janar na tarayya bisa zarginsa da almundahana ta naira biliyan 80.
Hukumar ce ta bayyana haka a shafinta na Facebook inda ta ce ta kama shi a ranar Litinin 16 ga watan Mayun 2022.
Hukumar na zargin Ahmed da karkatar da kuɗin ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi.
EFCC ta ce an yi amfani da kuɗin wurin gina rukunin gidaje a Kano da Abuja.
An kama Idris bayan ya ƙi karɓar gayyatar da EFCC ta rinƙa aika masa domin tuhumarsa kan zarge-zargen da ake yi masa, kamar yadda hukumar ta bayyana.