Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya nuna bacin ransa kan yadda aka saki ‘yan daba da ke kulle a jihar. Gwamnan ya ce wannan wani mataki ne na kawo tsaiko a kokarin da gwamnati ke yi na dakile matsalar dabanci a jihar.
Abba Kabir ya bayyana haka ne yayin tarbar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a gidan gwamnati. Ya bayyana yawan ‘yan dabar da aka kama domin yi musu hukunci amma abin takaici an sako su.
Har ila yau, gwamnan ya zargi jam’iyyun adawa da kokarin kubutar da ‘yan dabar domin biyan buƙatar kansu ta siyasa.
“Lokacin da muka zo gidan gwamnati, mun samu matsalolin tsaro da dama da suka hada da kwacen waya da fashi da kuma dabanci.” “Yan daba na saran mutane domin kawai su karbi wayoyinsu, amma cikin ikon Allah mun kawo karshen matsalar cikin watanni 10 da kusan kaso 90.”
“Abin takaici a karshen watan Ramadan, wasu matasa sun kutsa cikin masallaci a Dorayi tare da saran mutane da kuma sace wayoyinsu.”