Adamawa: An Damke Daliban Da Suka Kashe Wata Budurwa

Rundunan yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran kama wasu dalibai da kisan wata budurwa mai suna Franca Iliya wanda kuma dukkanisu dalubenai a kwaljin fasaha ta tarayya dake Mubi a jahar Adamawa.

Kakakin rundunan yan sandan jahar ta Adamawa D S P Suleiman Yahaya Nguroje ne ya tabbatarwa muryar yanci haka a ofiahinsa dake ahelkwatan rundunan dake yola.

D S P Suleiman Nguroje yace an samu nasaran kama wadanda ake zarginne biyo bayaran rahoton da auka samu wanda hakan yasa kwamishinan yan sandan jahar Adamawa CP Aliyu Adamu baiyi da wasaba inda ya bada umurnin gudanar da bincike dangane da lamarin.

Daya daga cikin wanad ake zargin mai suna Abubakar wandama ahine saurayin yarinya kuma dalibine a kwalejin fasaha ta tarayya a garin Mubi ya tabbatarwa muryar yanci cewa cikin ya shiga tsakaninsu da budurwr taahi wanda haka yasa suka yanke shawaran zubar da cikin, hakan yasa ya kiran wani dalibi mai suna Huzaifa Shuaibu wanda ya karantu magunguna a makarantar kiwon lafiya a garin na Mubi.inda shi kuma yayi mata aluran domin cikin ya zube amam sai ta rasa ranta. Sakamokon haka ne sai suka kira Rabi u Adamu wanda shima dalibine a kwalejin fasaha ta tarayya domin binneta a bayan kwalejin.

Acewar kakakin rundunan yan sandan dai wadanda ake zargin suna sahin biciken manyan laifuka kum da zaran sun kammala bincike zasu gurfanar dasu gaban kotu domin su fuskanci shariya.

Suleiman Nguroje ya kirayi al umma dake fadin jahar da kada auyi kasa a gwiwa su rinka gaggauta taimakawa rundunan da bayanai da zai taimaka wajen kama masu aikata laifi a fadin jahar baki daya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply