An Shawarci ‘Yan Najeriya Su Rungumi Noman Auduga – Shugaban Manoman Auduga

An bayyana cewa noman auduga abune dake yake da mutukàn muhimmanci a fadin Najeriya don haka an shawarci al umma a Najeriya da su maida hankali wajen noman auduga domin bunkasa masana antu a fadin kasan baki daya.

Shugaban kungiyar manoman auduga jahar Adamawa Alhaji Muhammed Saleh Gwalan ne ya baiyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a yola.

Muhammed Saleh gwalan yace daga cikin abunda ake yi da auduga sun hada da saka, yin tufafi, yin mai da dai sauransu.

Ya kuma kirayi gwamnatin tarayya dana jihohi har dana na kananan hukumomi da auma sukasance masu tallafawa manoma auduga a Najeriya domin bunkasa harkokin noman auduga a fadin Najeriya baki daya.

A cewar shugabàn kungiyar manoman audugan dai noma audugan zaitaimaka wajen samar da aikinyi a tsakanin matasa harma da bunkasa tattalin kasa.

Da wannan ne yake shawartan matasa da suma su ahiga a dama dasu wajen gudanar da harkokin noman audugan.

Labarai Makamanta

Leave a Reply