2023: Atiku Ne Mafita Ga ‘Yan Najeriya – Matar Atiku

A daidai lokacin da jam’iyyar PDP ta tsaida tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyar, ita kuwa Mai dakinsa hajiya Ruƙayya Atiku Abubakar ta yaba wa shugabanin jam’iyar da kuma ‘ Ya’yan jam’iyyar baki daya da suka zabi cancanta na zaben Mai gidan ta a matsayin ɗan takarar shugaban kasa.

Hajiya Ruƙayya ta bayyana hakan ne lokacin da take zantawa da manema labarai a Abuja dangane da halin da al’ummar Nijeriya ke ciki inda ta ce matuƙar alummar Nijeriya suka zabi Wazirin Adamawa a zaben 2023 za su samu saukin rayuwa a fannoni daban daban.

Da take ƙarin haske dangane da kalubalan tsaro kuwa Rukayya ta ce kamar yadda ta san Maigidan ta da jajircewa akan abu tana da tabbacin zai sharewa ‘Yan Nijeriya hawaye.

Daga karshe tayi kira ga ‘yan Nijeriya da su tabatar sun mallaki katin zabe domin hakan ne zai basu damar kaɗa kuri’un su a lokacin zabe, kana ita kuma hukumar zabe ta taimaka ta ƙara wa’adin gudanar da aikin yi wa ‘yan kasa katin zaben.

Labarai Makamanta

Leave a Reply