?ungiyar kare al’adun Fulani a Najeriya ta Miyetti Allah ta ce an kashe makiyaya a?alla 10,000 tare da raba wasu miliyan biyu da muhallansu a fa?in ?asar cikin shekara bakwai da suka wuce.
Bayanan sun fito ne bayan wani taro kan tsaro da ?ungiyar ta shirya tare da ha?in gwiwar ?ungiyar Northern Consensus Movement (NCM) ta ‘yan Arewa sakamakon matsalolin tsaro da suka ce Fulani na fuskanta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito ranar Asabar.
Cikin wata sanarwar bayan taro a ranar Juma’a, ?ungiyar ta ce daga 2015 zuwa yanzu makiyaya da dama sun fuskanci matsaloli, inda aka sace ko kashe dabbobi fiye da miliyan hu?u.
“Yi wa Fulani ba?in fenti da nuna musu tsana da kuma rura wutar ?abilanci a kan su da kafofin ya?a labarai ke yi ka iya kaiwa ga kisan ?are-dangi,” in ji sanarwar.