Za Mu Sako Tubabbun ‘Yan Boko Haram Cikin Al’umma – Gwamnatin Tarayya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar hukumomi sun kammala shirin miƙa wasu mayaƙan Boko Haram fiye da 600 da suka tuba ga gwamnatocin jihohinsu domin shigar da su cikin sauran al`umma.

Hedikwatar tsaro ta ƙasa ta bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne bayan an shigar da su cikin wani shirin gyara hali.

Hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Lucky Irabor ya bayyana cewa an kammala shirin miƙa mayakan Boko Haram ɗin da suka tuba su 613, bayan an gyara musu hali.

Ya yi bayanin ne a wajen wani taron masu hannu ko ruwa da tsaki a ƙarƙashin tsarin nan na ba da damar miƙa wuya ko tuba ga mayaƙan Boko Haram, wato Operation Safe Corridor.

Ya ce za a mika su ne ga jihohinsu na asali domin shigar da su cikin al`umma, kuma a halin da ake ciki ana gab da kammala aikin sauya musu tunani da zare musu tsattsaurar akida.

A cewar Hafsan hafsoshin, tubabbun mayakan Boko Haram ɗin na bukatar kulawa sosai a wannan gaɓa ta gyara hali da sake shiga cikin jama`a, don haka sai jihohin sun tsaya sosai a kan su.

Janar Irabor ya ce idan aka zo sallama ko yaye tsoffin ƴan Boko Haram din, za a ba su guzurin kayan abinci da kayan zaman gida da kuma kayan aiki irin sana’ar da suka koya don fuskantar gangariyar rayuwa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply