Yakin Rasha Da Ukraine Zai Haifar Mana Da Annoba – Dangote

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya gargadi yan Najeriya cewa kowa yayi tanadi kuma a kwana da shirin tsindumawa cikin karancin abinci da tsananin yunwa nan da watanni biyu masu zuwa.

Dangote ya ce dole gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci, masana;antu da noma su zauna a tattauna yadda za akawo karshen wannan matsala .

Ya kara da cewa tun yanzu an fara samun hauhawan farashin abubuwa kamar Taki, Masara, Alkama da dai sauran su.

” Za a samu karancin Masara da alkama a duniya saboda yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine. Wadannan kasashe sune ke samar da kashi 30 cikin 100 na uria da ake yin takin zamani da shi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply