Tsaro: Sama Da Mutum 20,000 Sun Yi Batan Dabo A Arewa

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce sama da mutum 20,000 ne suka yi sama ko kasa saboda rikicin da ke faruwa a arewa maso gabashin Najeriya.

ICRC ta ce yakin wanda aka shafe shekara 12 ana yi ya sa an yi asarar dubban rayuka, kuma miliyoyi sun rasa matsugunansu.

A wani taron masu ruwa da tsaki da take gudanarwa a Maiduguri, ICRC ta ce ta yi rijistar sama da mutum 20,000 da suka ɓata a arewa maso gabas, kuma suna fargabar cewa ko dai sun tsere ko kuma an kashe su.

“A karamar hukumar Bama kawai mun yi rajistar mutum 4,000 da ba a san inda suke ba a halin yanzu”, in ji Usman Kunduli Bukar na kungiyar ta Red Cross.

Labarai Makamanta

Leave a Reply